HAUSA NEWS

Wasu Iyaye Na Mika ‘Ya’yansu Don Kunar Bakin Wake – Inji Kukasheka

KUKASHEKA

A hirar da yayi da Muryar Amurka Kakakin sojojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya ce wasu iyaye a shiyar arewa maso gabashin kasar na mika ‘ya’yansu ga kungiyar Boko Haram domin yin anfani dasu a kunar bakin wake.

Yana mai cewa an sami wasu iyaye da suke ganin mika ‘ya’yansu da suka haifa wata hanya ce ta taimakawa aikin Boko Haram na masha’a. ‘Yan ta’addan sai su hure ma ‘ya’yan nasu kunne har su kai ga aikin kunar bakin wake.

Masanin kimiyar zamantakewar jama’a Farfasa Muhammad Tukur Baba Iyan Mutum Biyu wanda yanzu yake bincike mai zurfi na sabon salon anfani da yara da kungiyar Boko Haram ke yi ya yi bayani kadan daga cikin abubuwan dake jawo hakan.

A cewarsa, na daya idan mutum ya yi imani da wata akida babu abun da ba zai iya yi ba a kanta. Na biyu irin sakon da ‘yan ta’adan ke bada wa yana shiga cikin kunnen mutane musamman idan ana yinsa yau da kullum har ya shiga mutum. Wani abun kuma shi ne yin imani da abun da ba daidai ba saboda sabo da dadewa dashi. Wadannan abubuwan sukan sa mutane su yi imani da abun da ba haka yake ba.

Farfasa Tukur Baba ya bada shawara akan abun da yakamata a yi. Akwai hanyoyin shawo kan ta’addanci. Gwamnati zata yi nata. Shugabanni zasu yi nasu kana jama’a ma zasu yi nasu.

Advertisements

Categories: HAUSA NEWS