HAUSA NEWS

Obasanjo, Yar’Adua da Jonathan sun barnatar da Triliyan 11 inji SERAP

OBJ & JO

Kungiyar Tabbatar da gaskiya ta SERAP a Najeriya ta zargi Gwamnatocin Olusegun Obasanjo da Umaru Yar’Adua da kuma Goodluck Jonathan da barnatar da Naira triliyan 11 da sunan samarwa kasar wutar lantarki amma kuma daga bisani sai aka bar ‘yan kasar da sayen duhu.

Wani bincike da kungiyar ta gudanar ya nuna mata cewar cin-hanci da rashawa da almundahana sun dabai-baye harkar samar da wutar, abinda ya sa aka kashe makudan kudade ba tare da samun hasken wutar ba.

Farfesa Yemi Oke na Jami’ar Lagos ya gabatar da rahotan binciken, a karkashin jagoran shugaban SERAP Barrister Femi Falana wanda ya zargi gwamantocin da abokan huldar su da suka saye kamfanonin wutar da tilastawa ‘Yan Najeriya biyan duhu maimakon wutar da suke bukata.

Advertisements

Categories: HAUSA NEWS