HAUSA NEWS

Najeriya da Somalia da Sudan ta Kudu da Yemen na kukan Yunwa

YUNWA

Majalisar Dinkin Duniya ta sake gargadin cewar yanzu haka akalla Mutum miliyan 20 ke fuskantar barazanar Ukubar yunwa sakamakon yaki a kasashen Najeriya da Somalia da Sudan ta kudu da kuma Yemen.

Kwamitin Sulhu na Majalisar ya bayyana damuwa kan kuncin da wadanan mutane ke ciki, musamman abinda ya shafi tallafin gaggawa da kuma magance matsalar baki daya.

Jami’in jinkai na Majalisar ya ce Dala biliyan 2 da rabi kawai aka samu daga gidauniyar kusan Dala biliyan 5 da aka kaddamar domin taimakawa wadanan kasashe.

A cewar Majalisar rashin bada taimako a kan lokaci na iya barazana ga rayuwa miliyoyin mabukatan.

Advertisements

Categories: HAUSA NEWS