HAUSA NEWS

Amurka ta mai da martini kan Korea ta Arewa

TRUMP

A yayin da Korea ta Arewa ta yi barazanar kaddamar da farmaki kan yankin Guam na Amurka da ke tekun Pacific, shugaba Donald Trump ya ce, Amurka ta mallaki makamin nukiliya mai karfin da ya zarce wanda ta ke da shi a baya.Kalaman shugaban Amurka Donald Trump na a matsayin barazana ga Korea ta Arewa wadda ta ce, ta na duba yiwuwar kai wa Amurka farmaki makami Nukilyan a yankin Guam na kasar da ke tekun Pacific.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaba Trump ya ce, makamin Nukiliyar sojin Amurka na da karfin da ya zarce wanda suka mallaka a can baya.

Shugaban ya ce, umarnin da ya fara bayarwa a matsayinsa na shugaban kasa, shi ne inganta makamin Nukilyar kasar.

Sai dai a cewarsa, ba sa fatar amfani da wadannan shu’uman makaman, amma ya jaddada cewa, har yanzu Amurka ce kasa mafi karfi a duniya baki daya.

Tuni dai Babban jami’in diflomasiyar Trump, Rex Tillerson ya aike da sakon kwantar da hankali ga mutanen yankin na Guam bayan wannan barazana ta Korea ta arewa.

Zafafen kalaman Trump kan wannan al’amari sun fito da yadda Amurka ta fusata game da matakin da Korea ta Arewa ke dauka na gwaje-gwajen makamin Nukilya, yayin da China da wasu kawayen Amurka suka bukaci bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.

Advertisements

Categories: HAUSA NEWS